[LYRICS] Boc Madaki – Yawo ( Prod By C-Man)

YAWO Lyrics By B.O.C(@BOCMadaki
[INTRO]
Ji Mana,Ku Tsaya Guys!!! 
[CHORUS]

Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne 

Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne 

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne

-Lallai Kana Da Yawo!

(Jama’a Suka Ce Mun) 

-Lallai Kana Da Yawo 

(Gayu Na Suka Ce Mun)

-Lallai Kana Da Yawo 

(Babyn Chan Ta Ce Mun) 

-Lallai Kana Da Yawo 


[VERSE ONE

*What! 

*Da Muddun Na Bude Kofa,Na Shiga Mota 

*Bayan Direba Ya Anshi Boza 

*Kan Tafiya Ta Tabbata Da Addu’a Na Kan Soma 

*Domin Sai Da Rai A Kan Ci Oba 

*Ya Rabbi,Gatan Yara Da Manya 

*Makiyayin Mu Da Dare,Safe,Rana Da Yamma 

*Sa’in Da Muke Tafiye-tafiye Ka Kiyaye Mana Hanya 

*Gotta Get There Don Kar In Bar Iyaye Na Da Anya

*Da Kiran Abokai Na A Waya Duk Don Su San Ya 

*Don Shi Ne Daya Daga Cikin Muhimmancin Kusanya 

*Bari Duk Wani Barawo Kar Ya Gan Mu 

*Kuma Duk Wani Tafiyan Da Muka Yi Mu Kai Da Ran Mu 

*Amen! Babu Abun Da Zan Ce Sai Dai Amin 

*Don Kamin Ma In Tambaya Uba Na Yana Min…

-…Kyawawan Abubuwa

*Kamar Bari Na Da Rai Da Sama Mun Batutuwa….

*….Na Fada Wanda Dan Adam Bai Tada Mun A Kunnuwa 

*In Dakata? Su Din Su Wa? 
[CHORUS]

*Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne 

*Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne 

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne

-Lallai Kana Da Yawo!

*(Gyatuman Chan Ta Ce Mun) 

-Lallai Kana Da Yawo 

*(Dattijon Nan Ya Ce Mun)

-Lallai Kana Da Yawo 

*(Mallam Hassan Ya Ce Mun)

-Lallai Kana Da Yawo


[VERSE TWO]

*Komin Nisan Garin Ku Ku Shirya Don Muna Zuwa 

*Gara Mu Gaji,Mu Huta,Mu Tashi Da Mu Hakura 

*Don Da Hutu Ainun Bayan Mun Samu Babu Takura 

*Ga Ayawo,Ku Ce Wa Gayu Su Taru Fa 

*Ga Wuta,Toh Me Zai Hana Chasun Mu Faruwa 

*Gyatuma Ta Tana Mun Fata In Samu Gata A Rayuwa Ta 

*Da Na Ce ‘Amin’ Sai Na Ga Ko Ina Babu Rata 

*Kuma Karya Ne Rashin Arziki Ya Sa Mu Sata 

*In Har Na Taba Karaya A Da Yau Da Liver Na Dawo *Wasika Na Kawo 

*Sakon Da Ya Kunsa Shi Ne Yanzu Da Riba A Yawo 

*Tunda Kunnuwa Na Taimaka Wa Basiran Makaho 

*Mallam In Ka Tsani Kiwuya Sai Ka Diba Wa Yaro 

*Ka Mika A Baho 

*Domin Sai Iska Na Kadawa A Ke Shika Da Daro 

*Abun Kashedi,Ba Na Hira Da Tabo 
[CHORUS] 

*Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne 

*Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne 

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne

-Lallai Kana Da Yawo!

*(Aboki Na Ya Ce Mi Ni) 

-Lallai Kana Da Yawo 

*(Kawa Ta Ta Ce Mi Ni)

-Lallai Kana Da Yawo 

*(Mabiya Na Suka Ce Mi Ni ) 

-Lallai Kana Da Yawo
[VERSE THREE]


*On My Way To A Destination Where My Destiny Leads 

*I’ve Seen So Many Nights With My Eyes Open 

*Survival Warfare,No Man Alive Is Resting In Peace *Tryna Make Something Real Outta All The Lies Spoken 

*Na Ga ‘No’,Na Ga ‘Biyayya’ 

– Na Ga ‘So’,Na Ga‎ ‘Kiyayya’ 

*I’ve Seen Love And Hate,I’ve Seen Curve And Straight 

*I’ve Seen Flop And Great,I’ve Seen Lords And Slaves 

*I’ve Seen The Highs And Lows,I’ve Seen The Thighs And Toes

*Mallam Bar Ganin Ina Ta Hada Zufa 

*Sai Na Kai Inda Ba Wanda Ya Taba Zuwa 

*Fiye Da Jirgi Da Radio,Cike A Titi Da Stereo 

*Daba Daba Daban Daban,Tasha Tasha A Chan Da Nan 

*Mun San Hanyan Ba Kyau Amma Daga Kafa Alambaram 

*Always On The Road,Har Na Saba Da Gargada 

*Ai Cin Boris Ya Fi Kyau In Ka Chaba A Jar Kasa 

*Na Dawo Lafiya,Ga Saraba Ku Raba 

*Yau Yau Zan Koma In Ta Kama,Ko Da Kafa Mu Gwada 

 

[CHORUS
*Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne 

*Kyan Yawon Ba Tafiya Ba Ne,Dawowa Ne 

-Kyan Yawon Bayarwa Da Tarowa Da Kawowa Ne

-Lallai Kana Da Yawo!

*(Mutanen Bauchi Suka Ce Mun) 

-Lallai Kana Da Yawo

(Mutan Arewa Suka Ce Mun)

-Lallai Kana Da Yawo

(Duk Nigeria Suka Ce Mun)

-Lallai Kana Da Yawo 

DOWNLOAD THE TRACK

Leave a Response

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.