BARAYI SUN JE GIDAN BMERI ABOKI BAYAN BARIN SA LAGOS A JIYA.
A jiyane damisalin karfe uku na dare barayi su kimanin mutun bakwai suka yi yunkurin sata ta hanyan pasa gidan shahararran mawakin Hausa Hip Hop din mazaunin jahar Lagos wato Bmeri Aboki bayan awowi goma sha biyar daya baro Lagos zuwa jahar Kano daurin aure, wasu makwaptan da karar pasa kofar gidan ya tashe su daga barci ne suka baiyanawa majiyar mu cewa sunji hayaniya dakuma kara daga gidan mawakin, inda hakan yajawo hankalin su domin sunce sun san mawakin yayi tafiya amma iyalan sa suna cikin gidan, dan haka suka kai agaji gidan inda barayin suka ranta a na kare. Zuwa yanzu dai hukumar yan sandar ungwar mawakin suna binciki domin gano suwaye bayayin, mun kuma naimi muji tabakin mawakin daga Kano, sai dai management dinsa zunce bazai ce komai ba yanzu. Amma sun tabbatar mana cewa iyalan mawakin suna cikin koshin lafiya. Zamu sanar daku akan halin da akeciki dazaran wani abu sabo ya bujiro akan wannan maganar.Allah kiyaye.