WASIKA ZUWA SAMA(Lyrics)
CHORUS
Mutuwa(4x)
VERSE ONE
*Baba, Mutuwar Ka Bai Zo Mana Da Sauki Ba
*Abun Takaicin Ma
*Shi Ne Da Mun Wuce Mutan Anguwa Suna Hira
*Maimakon Mun Jaje Da Tausaya Wa Yanayi Na
*Sai Ka Ji Sun Ce Na Chacchanci Azaban Da Ke Bi Na
*Kullum Mama Tana Cikin Tunani, Sun Ki Barin Ta Ta Huta, Suna Ta Kiran Ta Maiya
*Ba Fada Mun Aka Yi Ba Na Ji Na Gani Da Kai Na
*Ya Zan Yi Da Rai Na
*Duk Da Dai Da Sanin Mu Cewa Da Kudin Ka Ka Gina
*Baba Karami Sun Zo Sun Kore Mu Sun Sai Da Gidan
*Wai Don Mama Ba Ta Taba Haifan Yaro Na Miji Ba
*Kuma A Al’adan Ku Ba A Raba Gado Da Iri Na
*Sai Ka Ce Ni Na Hallaci Kai Na ‘Ya Mace
*Ashe,Rayuwar Wassu Marayu Haka Ne
*I’m In Pain Hoping For Better Days
*While I Pray You Are In A Better Place
CHORUS
Mutuwa(4x)
VERSE TWO
*Mama,Mutuwar Ki Ya Bar Mu Cikin Azaba
*Ba Mu Samun Kula A Kan Kari Yadda Muka Saba
*Barin Ma An Daina Sa Mana Abincin Mu Da Nama
*Mun Daina Zuwa Makaranta Don Bamu Samun Dama
*Daga Dan Gaban Goshin Ki Yanzu Ni Ne Bawar Gidan
*An Sallami Baba Mai Aiki, Ni Ne Na Mai Da Gurbin Ta Sai Dai Ni Din Ba A Biya
*Da Safe Ni Na Kan Riga Kowa Tashi
*Da Dare, Kowa Ya Kan Riga Ni Barci
*Kanne Na Duk Sun Koma Zama Da Kawu A Kauye
*Duk A Bayan Mutuwar Ki Don Baba Ya Sake Aure
*Mun Yi Matukar Rashi
*Fiye Da Manomin Da Bayan Damina Mai Albarka Wuta Ya Kone Masa Hatsi
*Oh Mutuwa! Ya Sace Mu Wane Dan Fashi
*Da So Shi Ne Samu,Ki Dawo Rayuwa Ko Na Minti Daya In Gan Ki
*Wasika Daga Dan Ki
CHORUS
Mutuwa(4x)
VERSE THREE
*Da Na Makadaici
*Mutuwar Ka Ya Faru Ne Kamar A Mafarki
*Ko Zan Gan Ka A Raye In Na Farka Daga Barci
*Ka Tafi Ka Bar Mutan Duniya Na Ta Mun Habaici
*Kullum Ina Cikin Tamabaya,Shin Ta Wani Hanya Na Yi Wa Rayuwa Laifi
*Ji Nake Kamar Ni Ne ‘Yar, Kai Ne Mahaifi
*Da Safe In Zan Fita Wa Zai Ce Mun Sai Anjima,
-Wa Zai Ce Mun Maraba In Na Dawo Da Maraici
*Wa Zai Haifa Mini Jika?
*Wai Zai Ce Mun Yana So? Wa Zai Karba In Na Mika?
*Tunda Mahaifin Ka Ma Ba Ya Nan Wa Zai Mini Hira
*Wai Karfafa Ni,Wa Zai Gina Mini Gida
*Tun Ranar Da Na Haife Ka Na San Zaka Zamo Soja
*Har Hakan Ya Zamo Gaske
-Ka Yi Nasara A Yakin Farko,Ka Dawo… Daka Koma
*Labarin Mutuwan Ka Ne Ya Kwankwasa Mini Kofa
*Wish I Stopped The Bullet
*Wish I Had Made The Trigger Disappear Before They Pull It
CHORUS
Mutuwa(4x)